Lahadi 12 Yuli 2026 - 16:21
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (54) | Mahdawiyya A Littattafan Ahlus Sunna

Hauza / Da nazarin littattafan hadisan Ahlus-Sunnah, a fili yake cewa batun Mahdawiyya ya samu kulawa sosai a cikinsu. Baya ga dimbin ruwayoyin da suka zo a warwatse cikin littattafansu, rubuce-rubuce da aka keɓe musamman kan Imam Mahdi (A.S.) da malaman Ahlus-Sunnah suka wallafa suna nuna irin matsayi mai girma da akidar Mahdawiyya take da shi a wajensu.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, ana gabatar da jerin darussan Mahdawiyya mai taken "Zuwa ga Al'umma Mai Manufa", domin yada koyarwa da ma'arifar da suka shafi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa).

Mahdawiyya a cikin Littattafan Ahlus-Sunnah

Imani da Mahdawiyya da kuma bayyanar Imam Mahdi (A.F), sabanin yadda wasu suke zato, ba akida ce ta Shi'a kaɗai ba. A'a, tana daga cikin muhimman akidun Musulunci da suka samo asali daga busharorin Manzon Allah (SAWA), kuma dukkan mazhabobin Musulunci sun yarda da ita.

A cikin batutuwan akida, kaɗan ne daga cikin batutuwan da suka samu irin wannan muhimmanci.

Hadisan da suka shafi Imam Mahdi (A.S.) sun zo a cikin shahararrun littattafan Ahlus-Sunnah. A mafi yawan waɗannan littattafai an yi bayani kan siffofinsa, rayuwarsa, alamomin bayyanarsa, wurin bayyanarsa da mubaya'a, yawan mataimakansa da sauran batutuwa.

Abin da ya shahara a tsakanin Musulmi tun tsawon tarihi shi ne cewa a ƙarshen zamani wani mutum daga Ahlul Baiti (A.S.) zai bayyana, ya cika duniya da adalci, Musulmi za su bi shi, kuma zai shugabanci ƙasashen Musulunci. Sunansa Mahdi ne. (Abdurrahman Ibn Khaldun, Muqaddimat al-'Ibar, shafi na 245).

Sai dai wasu kaɗan sun ƙi yarda da asalin akidar Mahdawiyya, suna ƙoƙarin musunta ta da hujjoji marasa ƙarfi, suna kuma cewa akida ce ta Shi'a.

Amma idan aka duba littattafan hadisan Ahlus-Sunnah, za a ga cewa batun Mahdawiyya ya zo da yawa. Haka kuma rubuta littattafai na musamman game da Imam Mahdi (A.S.) da malaman Ahlus-Sunnah suka yi yana tabbatar da girman wannan akida a wajensu.

Littattafan Ahlus-Sunnah kan Mahdawiyya sun kasu gida biyu:

1. Littattafan Hadisi na Bai-ɗaya

A cikin waɗannan littattafai an ambaci Mahdawiyya tare da sauran batutuwan addini. An kawo ruwayoyi da ke tabbatar da cewa Imam Mahdi (A.S.) yana daga zuriyar Manzon Allah (SAWA), daga zuriyar Imam Ali (A.S.) da Sayyida Fatima (A.S.), tare da bayanin siffofinsa, rayuwarsa, yadda zai bayyana da yadda mulkinsa zai kasance.

Daga cikin fitattun littattafan akwai:

Al-Musannaf na Abdur Razzaq bn Hammam as-San'ani (ya rasu 211H). Ya buɗe babi mai suna "Babul Mahdi", inda ya kawo fiye da hadisi goma game da Imam Mahdi. Wannan shi ne littafin farko daga Ahlus-Sunnah da ya tattara hadisan Mahdi cikin tsari.

Kitab al-Fitan na Nu'aym bn Hammad al-Marwazi (229H). Ya kawo ruwayoyi masu yawa game da Imam Mahdi (A.S.), siffofinsa da abubuwan da za su faru a zamaninsa. Littafin ya kasu kashi goma, kuma mafi yawan hadisan Mahdawiyyah suna cikin sashe na biyar da abin da ya biyo bayansa.

Al-Musannaf fi al-Ahadith wa al-Athar na Abdullah bn Abi Shaybah (235H). A cikin babin Al-Fitan ya kawo hadisan da suka shafi Mahdi (A.S.), ciki har da nasabarsa, halayensa, tsawon mulkinsa, yanayin kafin bayyanarsa da alamomin bayyanarsa.

Musnad Ahmad na Ahmad bn Hanbal (241H), daya daga cikin manyan limaman Ahlus-Sunnah. Ya ƙunshi hadisan Mahdawiyya da dama, kuma shi ne daga cikin tsofaffin littattafan hadisi da suka fi tattara hadisan Mahdawiyya.

Sunan Ibn Majah na Muhammad bn Yazid al-Qazwini (275H). A cikin Kitab al-Fitan ya ware babi mai suna "Bab Khuruj al-Mahdi".

Sunan Abi Dawud na Abu Dawud as-Sijistani (275H). Ya ware wani sashe na musamman mai suna "Kitab al-Mahdi", wanda yake daga cikin muhimman tushe na Mahdawiyya a wajen Ahlus-Sunnah.

Al-Jami' as-Sahih (Sunan at-Tirmidhi) na Imam Tirmidhi (279H). Duk da cewa hadisan Mahdi a cikinsa ba su da yawa, amma suna da ingantattun isnadai kuma suna ɗauke da muhimman bayanai.

Al-Mustadrak 'ala as-Sahihayn na Hakim Nishaburi (405H). Ya kawo hadisan Mahdi a babin Al-Fitan wa al-Malahim da wasu wurare daban-daban, yana bayani kan nasabarsa, siffofinsa, yanayin kafin bayyanarsa da sauran batutuwa.

Kanz al-'Ummal fi Sunan al-Aqwal wa al-Af'al na Ali al-Muttaqi al-Hindi (975H). Baya ga ruwayoyi da ya kawo a wurare daban-daban, ya ware babi mai suna "Khuruj al-Mahdi", inda ya tattara dimbin hadisai daga tushe daban-daban.

2. Littattafan Hadisi da Aka Keɓe wa Imam Mahdi (A.S.)

Kamar yadda malaman Shi'a suka yi, malaman Ahlus-Sunnah ma ba su tsaya kan ruwayoyin da suke cikin sauran littattafai ba; sun rubuta littattafai na musamman game da Imam Mahdi (A.S.). Daga cikinsu akwai:

Arba'una Hadithan na Abu Nu'aym al-Isfahani (420H). Koda yake ba a samun wannan littafi a yau, amma Arbali ya kawo cikinsa gaba ɗaya a cikin Kashf al-Ghummah fi Ma'rifat al-A'immah.

Al-Bayan fi Akhbar Sahib az-Zaman (A.S.) na Muhammad al-Ganji ash-Shafi'i (658H). Ya tattara hadisai kusan saba'in cikin babuka 25, kuma ya bayyana cewa ya kawo hadisai ne daga hanyoyin Ahlus-Sunnah kawai domin nuna cewa Mahdawiyya ba akidar Shi'a kaɗai ba ce.

Abin lura shi ne cewa, duk da yawancin malaman Ahlus-Sunnah sun ƙaryata haihuwar Imam Mahdi (A.S.), marubucin wannan littafi ya sanya babi na ƙarshe da taken: "Fi ad-Dalalah 'ala Jawaz Baqa' al-Mahdi Hayyan"

"Hujja kan yiwuwar Mahdi ya ci gaba da kasancewa a raye." Wannan yana nuna cewa ya amince da haihuwar Imam Mahdi (A.S.) da kuma tsawon rayuwarsa.

'Iqd ad-Durar fi Akhbar al-Muntazar na Yusuf bn Yahya al-Maqdisi ash-Shafi'i (658H). Littafi ne mai faɗi kuma ya zama tushen marubutan da suka zo bayansa. Marubucin ya bayyana cewa ya rubuta shi ne saboda ya nuna cewa fitintinu da lalacewar zamani ba za su ci gaba har abada ba, domin za su ƙare da bayyanar Imam Mahdi (A.S.).

Al-'Urf al-Wardi fi Akhbar al-Mahdi (A.S.) na Jalaluddin as-Suyudi (911H). Ya tattara hadisai masu yawa game da Imam Mahdi, ya kuma ƙara wasu ruwayoyi da ba su cikin tarin Abu Nu'aym.

Al-Burhan fi 'Alamat Mahdi Akhir az-Zaman na Ali al-Muttaqi al-Hindi (975H). Wannan yana daga cikin manyan littattafan hadisi kan Imam Mahdi (A.S.), kuma ya ƙunshi fiye da hadisai 270.

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat" na Khudamurad Salimiyan tare da ƴan gyare-gyare kaɗan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha